Ubangiji Allah, ga mu nan gabanka - Littafin Wakoki 001. Holy, Holy, Holy
1) Ubangiji Allah, ga mu nan gabanka.
Tun da farin hasken safe, mu ke nemanka.
Muna yabon sunanka, ya Mai Iko Duka,
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
2) Ubangiji Uba, kai ne farkon kome,
Kai ka ba da ÆŠanka Yesu domin cetonmu.
Mu da muka tayar, kai ka ji tausayinmu.
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
3) Ubangiji Yesu, kai ne Almasihu,
Kai ka fanshi bayin ShaiÉ—an daga bautarsa.
Kai ka ba da jininka domin mu mutane.
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
4) Ubangiji Ruhu, sunanka Mai Tsarki,
Kai ne kana koya mana hanyar cetonmu.
Kai ne jagabanmu, kullum sai mu bi ka.
Muna sujada, ya Mai Tsarki.
5) Allah Ubangijinmu, É—aya cikin uku,
Harshe ba ya iya faÉ—in girman sunanka.
Uba, ÆŠa, da Ruhu, uku cikin É—aya,
Muna sujada, ya Mai Tsarki.