Ranan nan da ka bayar ta faɗi - Littafin Wakoki 23

Ranan nan da ka bayar ta faɗi - Littafin Wakoki 23

 Hausa hymnal book number 23 - Ranan nan da ka bayar ta faɗi - Littafin Wakoki 23. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Hausa Littafin Wakoki.Ranan nan da ka bayar ta faɗi - Littafin Wakoki 23

1) Ranan nan da ka bayar ta faɗi,

Kai ne ka sa duhu ya yi.

Mu rera waƙoƙi gare ka,

Yabonka kuwa zai tsarkake mu.


2) Mun gode don Ekklesiyarka,

Da himma ta ke shaidarka,

Tana kuwa kiwon dukan duniya,

Ba ta da hutu, ko kaɗan.


3) A ƙasashen duniya dayawa,

Hasken safe 'na ƃullowa,

Addu'a ba ta fasawa,

Yabo gare ka kullayaumin.


4) Loton da mu ke barci fa,

Waɗansu su ke farkawa,

Kowane lokaci, ƴaƴanka

Yabonka su ke furtawa.


5) Mulkinka ba zai shuɗe ba

Kamar su mulkokin duniya,

Amma ya tabbata da iko,

Har kowa ya bi nufinka.Hausa Anglican hymnal Littafin WakokiRanan nan da ka bayar ta faɗi - Littafin Wakoki 23

Hausa hymnal book number 23 - Ranan nan da ka bayar ta faɗi - Littafin Wakoki 23. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here Post a Comment (0)
Previous Post Next Post