Da yamman nan, ya Yesunmu - Littafin Wakoki 22

Da yamman nan, ya Yesunmu - Littafin Wakoki 22

Hausa hymnal book number 22 - Da yamman nan, ya Yesunmu - Littafin Wakoki 22. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Hausa Littafin Wakoki.Da yamman nan, ya Yesunmu - Littafin Wakoki 22

 1) Da yamman nan, ya Yesunmu,

Albarkaci maganarka,

Haskaka, Yesu, duhunmu

Bishe mu kuwa da Ruhunka.

Ya Yesunmu, mai taimako,

Ƙarfafa ranmu duka yau.

Ya Yesunmu, mai taimako,

Ƙarfafa ranmu duka yau.


2) Magaucinmu ya bi mu yau.

Da wayonsa, ya ruɗe mu.

Jaraba ma mai zafi ce,

Halinmu kuwa rarrauna ne.

Ya Yesunmu, mai nasara,

Ka cika mu da Ruhunka.

Ya Yesunmu, mai nasara,

Ka cika mu da Ruhunka.


3) Laifofinmu dayawa ne,

Tunaninmu miyagu ne,

Harshenmu duk da gurinmu,

Sun ƙara mana laifinmu.

Ya Yesunmu, yafe mu dai,

Da jininka, ka wanke mu .

Ya Yesunmu, yafe mu dai,

Da jininka, ka wanke mu.


4) Ya Ubangiji, Allahnmu,

Ka tsare mu da daren nan,

Da hannunka ka riƙe mu,

Da ikonka, ƙarfafa mu.

Ya Yesunmu, ka keƃe mu,

Har safiya, ka tsare mu.

Ya Yes…
Hausa Anglican hymnal Littafin WakokiDa yamman nan, ya Yesunmu - Littafin Wakoki 22

Hausa hymnal book number 22 - Da yamman nan, ya Yesunmu - Littafin Wakoki 22. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here Post a Comment (0)
Previous Post Next Post