Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami - Littafin Wakoki 12

Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami - Littafin Wakoki 12

Hausa hymnal book number 12 - Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami - Littafin Wakoki 12. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Hausa Littafin Wakoki.


Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami - Littafin Wakoki 12


1) Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami,
Mu yabe ka.
Kai ne Mahalicci, kai ne mai aminci,
Kai ne mafifici har abada.


2) Mun taru wurinka, kai ne madogara,
Mun yabe ka.
Kai ne mai ƙaunarmu, kai ne mai fansarmu,
Kai ne mai tsaronmu har abada.


3) Bayyana girmanka, nuna darajarka,
Kusance mu.
Tsarkake zukata, sauko da ikonka,
Furta maganarka, ya Allahnmu.


4) Mallaki ƴaƴanka, ƙarfafa bayinka
A duniyan nan.
Yi amfani da mu, kwaƃi ragwancinmu,
Mai da mu nan gaba manzanninka.
Hausa Anglican hymnal Littafin Wakoki


Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami - Littafin Wakoki 12

Hausa hymnal book number 12 - Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami - Littafin Wakoki 12. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post