Maɗaukakin Sarki madauwami ne - Littafin Wakoki 11

Maɗaukakin Sarki madauwami ne - Littafin Wakoki 11

Hausa hymnal book number 11 - Maɗaukakin Sarki madauwami ne - Littafin Wakoki 11 #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki.


Maɗaukakin Sarki madauwami ne - Littafin Wakoki 11


1) Maɗaukakin Sarki madauwami ne,
Kai ne kuma mafarin hikima duk.
Walƙiyar darajarka ta makanta mu,
Mai iko, mai nasara, ya Allahnmu.


2) Mulkinka mai haske ya tabbata nan,
A hankali, a natse saukowarsa.
Albarkarka tana zubowa kanmu,
Alheri mai yawa da nagartarka.


3) Kai ne mai rayad da talikanka duka,
Da lafiya da ƙarfi da iyawa kuwa.
Mun ga jamalinka cikin halitta,
Gwanintar aikinka ka bayyana kuwa.


4) Da rana da wata har taurari kuwa,
Kyawawan tafukka, da Kogin Kwara,
Da duwatsu duk da tuddai suna yi
Wa sunanka yabo, ya Mahalicci.


5) Ya Ubangiji mai girma, Mai Tsarki ne kai; .
Allah ne na zurfafa da al'arshi,
Mala'ikunka suna yin sujada,
Mu fa sai biyayya za mu yi maka.

Maɗaukakin Sarki madauwami ne - Littafin Wakoki 11Hausa Anglican hymnal Littafin Wakoki


Maɗaukakin Sarki madauwami ne - Littafin Wakoki 11

Hausa hymnal book number 11 - Maɗaukakin Sarki madauwami ne - Littafin Wakoki 11. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here Post a Comment (0)
Previous Post Next Post