Yinin nan ya wuce, dare yana bi - Littafin Wakoki 21

Yinin nan ya wuce, dare yana bi - Littafin Wakoki 21

Hausa hymnal book number 21 - Yinin nan ya wuce, dare yana bi - Littafin Wakoki 21. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Hausa Littafin Wakoki.


 

Yinin nan ya wuce, dare yana bi - Littafin Wakoki 21

1) Yinin nan ya wuce, dare yana bi,

Babu sauran haske, duhu yana yi.


2) Su taurari duka, aikin hannunka,

Su rundunan sama, suna walƙiya.


3) Yesu, Mai Alheri, sa albarkarka,

Bisa ƙanƙanana, yaran ƙaunarka.


4) Tsare mu da dare, inuwantad da mu,

Ta dalilin barci, ba mu ƙarfinka.


5) Yafe zunubanmu, wanke zukata,

Ba mu naka iko, gyarta ha1inmu.


6) Daga tarkon Iblis, daga wayonsa,

Algus, duk da ƙarya, ceci ƴaƴanka.


7) Duba masu ciwo, rage zafinsu,

Lura da marayu, ji addu'arsu.
Hausa Anglican hymnal Littafin WakokiYinin nan ya wuce, dare yana bi - Littafin Wakoki 21

Hausa hymnal book number 21 - Yinin nan ya wuce, dare yana bi - Littafin Wakoki 21. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here Post a Comment (0)
Previous Post Next Post