Ina misalan daraja da ban mamaki da - Littafin Wakoki 9

Ina misalan daraja da ban mamaki da - Littafin Wakoki 9

Ina misalan daraja da ban mamaki da - Littafin Wakoki 9

Hausa hymnal book number 9 - Ina misalan daraja a ban mamaki da, - Littafin Wakoki 9. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki 


1) Ina misalan daraja da ban mamaki da
Jamalinka ya bayyana, ya Allah, haskena!

2) Ya Allahna Madauwami, kwarjininka ya sa
In yi maka sujada fa a cikin zuciyata.

3) In ƙaunace ka kullum kuwa, mai iko duka ne,
Don ka yarda ka zo guna, ka nemi ƙaunata.

4) Ba wani uba na duniya, ba wata uwa kuwa,
Da za su iya renonmu yadda ka ke mana.

5) Sai abu ɗaya na ke so, in zauna gabanka,
In ga jamalin haskenka, in dinga sujada.

6) In yi shelar sunanka dai, in riƙa tunani
Yadda ka ƙaunace ni kuwa, ya Allah mai jinƙai.

7) Ina misalin daraja da ban mamaki kuwa
Na tsarin dukan hikima wadda ka ayana.


Hausa Anglican hymnal Littafin Wakoki


Ina misalan daraja da ban mamaki da - Littafin Wakoki 9

Hausa hymnal book number 9 - Ina misalan daraja a ban mamaki da, -   #Hausa Hymns #Littafin Wakoki . Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post