Ni na gaskata da Allah - Littafin Wakoki 16

Ni na gaskata da Allah - Littafin Wakoki 16

 Hausa hymnal book number 16 - Ni na gaskata da Allah - Littafin Wakoki 16. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Hausa Littafin Wakoki.


 Ni na gaskata da Allah - Littafin Wakoki 16

1) Ni na gaskata da Allah,

Ga shi, uku cikin ɗaya,

Uba, Ɗa da Ruhu kuma.

Allahntakarsu ɗaya.


2) Allah mai yin haskoki ne,

Shi Mahaliccinmu ne,

Har da duniya, duk da Sama,

Taurari da masu rai.


3) Allab Ɗa shi ya fanshe mu,

Shafaffe da Aikakke

Daga wurin Allah Uba,

Shi ne Hanya, Gaskiya, Rai.


4) Allah Ruhu Mai Tsarki kuwa,

Ba wurin da babu shi,

Ikon Allah a gare shi,

Shi Mai Tsarkakewa ne.


5) Allahntaka ga Triniti,

Ɗaya ne, ba uku ba,

Allahnmu Madauwami kuwa,

Gabansa mu rusuna.Hausa Anglican hymnal Littafin WakokiNi na gaskata da Allah- Littafin Wakoki 16

Hausa hymnal book number 16 - Ni na gaskata da Allah - Littafin Wakoki 16. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post