Ya Ubanmu, ka bishe mu - Littafin Wakoki 15

Ya Ubanmu, ka bishe mu - Littafin Wakoki 15

Hausa hymnal book number 15 - Ya Ubanmu, ka bishe mu - Littafin Wakoki 15. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Hausa Littafin Wakoki.


Ya Ubanmu, ka bishe mu - Littafin Wakoki 15


1) Ya Ubanmu, ka bishe mu
Cikin wannan duniya.
Kai kaɗai mai taimakonmu,
Dube mu da ƙaunarka.
Ba abin da za mu rasa,
In ka zama jigonmu.

2) Ya Mai Ceto, ka yi jinƙai.
Ka san kumamancinmu,
Kai ka sha wahalar giciye,
Domin fansar dukanmu.
Za mu jure har matuƙa
In ka sa albarkarka.

3) Sauko nan, ya Ruhun Allah.
Cika mu da ikonka.
Ba mu ƙauna da salama,
Murna marar iyaka.
Haka za mu ratsa duniya,
Har mu isa gidanka.


Hausa Anglican hymnal Littafin Wakoki


Ya Ubanmu, ka bishe mu- Littafin Wakoki 15

Hausa hymnal book number 15 - Ya Ubanmu, ka bishe mu - Littafin Wakoki 15. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post