Rana ta ubangiji ta sake zuwa yau - Littafin Wakoki 18

Rana ta ubangiji ta sake zuwa yau - Littafin Wakoki 18

Hausa hymnal book number 18 - Rana ta ubangiji ta sake zuwa yau - Littafin Wakoki 18. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Hausa Littafin Wakoki.Rana ta ubangiji ta sake zuwa yau - Littafin Wakoki 18

1) Rana ta ubangiji ta sake zuwa yau,

Hutawa domin jiki, ranar sujada ma.

A cikin taruwarmu, mun ta da muryarmu,

Mun gode maka, Allah, domin hutawarmu.


2) A ranan nan mai tsarki, 

Yesu, mai fansarmu, na ikonsa ya tashi, ya gama cetonmu,

Ya kwance sarkar Shaiɗan, ya tube ikonsa,

Ta wurin mutuwarsa, ya ka da mutuwa.


3) A ranan nan mai tsarki, Mai Taimako ya zo

A wurin Masu Binsa, ya zauna cikinsu.

Ya ba su ikon shaida, ya kau da tsoro duk,

Ya buɗe hankalinsu, ya eika zuciyarsu.


4) Mun gode maka, Allah, cikin alherinka,

Ka tuna da ƴan Adam, ka ba su hutu ma.

Ka taimake mu, Allah, mu tsare ranan nan

Har ran da za mu gan ka a cikin Sama can.Hausa Anglican hymnal Littafin WakokiRana ta ubangiji ta sake zuwa yau - Littafin Wakoki 18

Hausa hymnal book number 18 - Rana ta ubangiji ta sake zuwa yau - Littafin Wakoki 18. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here 


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post