Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka - Littafin Wakoki 20

Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka - Littafin Wakoki 20

Hausa hymnal book number 20 - Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka - Littafin Wakoki 20. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Hausa Littafin Wakoki.


Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka - Littafin Wakoki 20

1) Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka.

Kai ka kawo dukanmu yinin nan da lafiya

Muna rera waƙarmu, muna maka godiya.


2) In yau wata jaraba za ta kai mu haɗari,

Ba mu ikon jurewa, ƙara mana ƙarfi kuwa,

Kiyaye mu lafiya, har mu ka da zunubi.


3) Bisa ga maganarka, daidaita rayukanmu,

Bishe mu da Ruhunka, amshi mulkin nufinmu.

Bar mu miƙa gare ka hadaya ta zuciyarmu.


4) Ji yanzu addu'armu, ji mu, muna roƙonka.

Da mu duk da ƴanuwa, baiwarka mafificiya

Ita ce bukatarmu, sahihiyar zuciya.


5) Haka za mu bayyana yau da gobe godiyarmu.

Haka za mu ɗaukaka sunan Ubangijinmu.

Za mu shaida yabonka, Almasihu Allahnmu.Hausa Anglican hymnal Littafin WakokiYesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka - Littafin Wakoki 20

Hausa hymnal book number 20 - Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka - Littafin Wakoki 20. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here 


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post