Mu yi sujada ga Ubangiji - Littafin Wakoki 006

Mu yi sujada ga Ubangiji - Littafin Wakoki 006

 Mu yi sujada ga Ubangiji -  Littafin Wakoki 006

Hausa hymnal book number 6 - Mu yi sujada ga Ubangiji. - Littafin Wakoki 006. #Hausa Hymns #Littafin Wakoki. Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki 

1) Mu yi godiya domin ƙaunarsa.
Da zuciya ɗaya mu ɗaukaka shi,
Mu yabi sunansa da duk ladabi.

2) Mu yi tunani a kan girmansa,
Mu yi waƙoƙi kan alherinsa,
Mai Tsarki, Mai Ƙauna, Mai Gaskiya ne,
Mai ikon halitta, mai jin addu'a.

3) Bukatarmu duk shi ya ke ta biya,
Mu karƃe su fa tare da godiya.
Abinci, abin sha, numfashi da rai,
Lissafin kyautansa ya fi ƙarfinmu.

4) Mu raunana ne, amma cetattu,
Mu ƴaƴansa ne, bai yashe mu ba.
Yana marmari dai mu yi zumunta,
Jiƙansa mai yawa, ba misalinsa.

5) Al'amuranmu su girmama shi,
Da bakunanmu mu yi ta shaida.
Mu bauta masa, mu ji tsoronsa kuwa,
Gama shi ne Allah na duk duniya.





Hausa Anglican hymnal Littafin Wakoki


 Mu yi sujada ga Ubangiji -  Littafin Wakoki 006

Hausa hymnal book number 6 - Mu yi sujada ga Ubangiji -   #Hausa Hymns #Littafin Wakoki . Hausa Anglican hymnal #Anglican Littafin Wakoki. Follow our hymns here 
إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم